Isa ga babban shafi
Najeriya - APC

Sabbin shugabannin jam'iyyar APC ta kasa

Sabbin shugabannin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kasa: sanata Adamu amatsayin shugaba sai kuma Omisore, Sakatare Janar.

Alamar jam'iyyar APC mai Mulkin Najeriya
Alamar jam'iyyar APC mai Mulkin Najeriya © Bashir Ahmad
Talla

A yayin babban taron ta Na kasa da ta gudanar ranar asabar 26 ga watan Maris na 2022 jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta amince da ‘yan takara 54 da suka samu nasara.

Ga sunayen shugabannin da mukamansu:

(1) Abdullahi Adamu, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta yamma, a matsayin shugaban jam’iyyar ta kasa.

(2) Abubakar Kyari, Sanata daga jihar Borno a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar (Yankin Arewa)

(3) Emma Eneukwu (Enugu) a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar (Yankin Kudu)

(4) lyiola Omisore (Osun) a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa

(5) Fetus Fuanter (Plateau) a matsayin mataimakin sakatare jam’iyyar na kasa

(6) Muhazu Bawa Rijau (Niger) a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar (yankin Arewa ta tsakiya).

(7) Mustapha Salihu (Adamawa) mataimakin shugaban Jam’iyyar (yankin Arewa maso gabas)

(8) Salihu Lukman (Kaduna) a matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar (Arewa maso yamma).

(9) Ijeomah Arodiogbu (Imo) a matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar (Yankin Kudu maso kudu).

(10) Victor Ton Giadom (Rivers) a matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar (Yankin kudu maso gabas)

(11) D. I. Kekemeke (Ondo) a matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar (yankin Kudu maso yamma)

(12) Ahmed El-Marzuk (Katsina) a matsayin mai bada shawara a bangaren shari’a

(13) Uguru Mathew Ofoke (Ebonyi) a matsayin ma’ajin kudi na kasa

(14) Bashir Usman Gumel (Jigawa) a matsayin sakataren kudi na kasa

(15) Suleiman M. Argungun (Kebbi) a matsayin sakataren tsare-tsare na kasa

(16) Betta Edu daga Cross River, shugabar mata ta kasa

(17) F.N. Nwosu (Abia) a matsayin sakataren jin dadi da walwala na kasa

(18) Felix Morka (Delta) a matsayin sakataren yada labarai na kasa

(19) Abubakar Maikaf, Sanata daga Bauchi a matsayin mai binciken kudi na kasa

(20) Abdulahi Dayo Israel (Lagos) a matsayin shugaban matasa na kasa

(21) Tolu Bankole (Ogun) a matsayin shugaban masu bukata ta musamman – (Nakasassu)

(22) Ibrahim Salawu (Kwara) a matsayin mataimakin mai bada shawara kan shari’a na kasa

(23) Omorede Osifo (Edo) a matsayin mataimakin ma’aji na kasa

(24) Hamma-Adama Ali Kuro (Gombe) a matsayin mataimakin sakataren kudi na kasa

(25) Nzo Chidi Duru (Anambra) a matsayin mataimakin sakataren tsare-tsare na kasa

(26) Yakubu Murtala Ajaka (Kogi) a matsayin sakataren yada alamura na kasa

(27) Christoper Akpan (Akwa Ibom) a matsayin mataimakin sakataren walwala na kasa

(28) Olufemi Egbedeyi (Oyo) a matsayin mataimakin mai binciken kudi na kasa

(29) Zainab Abubakar Ibrahim (Taraba) a matsayin mataimakiyar shugabar mata ta kasa.

(30) Jamaluddeen Kabir (Zamfara) a matsayin mataimakin shugaban matasa na kasa

(31) Oluwatoyin Opawuye (Kwara) majalisar zartarwa (arewa ta tsakiya).

(32) Sirajo Dahuwa (Bauchi) majalisar zartarwa  (Yankin Arewa maso Gabas).

(33) Allyu Ahmed Yako (Kano) majalisar zartarwa  (yankin Arewa maso yamma)

(34) Aqunwa Anekwe (Anambra) majalisar zartarwa (yankin Kudu maso Gabas).

(35) Diriwari Akedewei (Bayelsa) majalisar zartawa ( yankin kudu maso kudu).

(36) Bunmi Oriniowo (jihar Ekiti) majalisar zartarwa (yankin kudu maso yamma).

(37) Yakubu Mohammed Adamu (Birnin Tarayya) a matsayin sakataren shiyya (yankin Arewa ta tsakiya).

(38) Mohammed Wali Shettima (Jihar Yobe) a matsayin sakataren shiyyar (Yankin Arewa maso Gabas)

(39) Bello Goronyo (Sokoto) a matsayin sakataren shiyya (Yankin Arewa maso yamma).

(40) Azobu Innocent Tapa (jihar Ebonyi) a matsayin sakataren shiyya (Yankin Kudu maso Gabas).

(41) Ita Udosen (Akwa Ibom) a matsayin sakataren shiyyar (Yankin Kudu maso kudu)

(42) Vincent Bewaji (Jihar Ekiti) a matsayin sakataren shiyya (Yankin Kudu Maso Yamma).

(43) Hadiza Aliyu (Jihar Kogi) a matsayin mai ba shiyya shawara kan harkokin shari’a (Yankin Arewa ta Tsakiya).

(44) Dauda Chakpo (Jihar Taraba) a matsayin mai ba shiyya shawara kan harkokin shari’a (yankin Arewa maso Gabas).

(45) Bashir Usaini Dutse (Jigawa) a matsayin mai ba shiyya shawara kan harkokin shari’a ( yankin Arewa maso Yamma).

(46) Mayor Ogbona Earnest (Jihar Ebonyi) a matsayin mai ba shiyya shawara kan harkokin shari’a (Yankin kudu maso Gabas).

(47) Isma’il Kolawole Majoro (Jihar Oyo) a matsayin mai ba shiyya shawara kan harkokin shari’a (Yankin kudu maso yamma).

(48) Ahmed Attah (Jihar Kogi) a matsayin sakataren shiyya (Arewa ta tsakiya).

(49) Abubakar Adamu Musa (Jihar Taraba) a matsayin sakataren shiyya (yankin Arewa maso Gabas).

(50) Salisu Uba (Zamfara state) a matsayin sakataren tsare-tsare na shiyya(Yankin Arewa Maso Yamma).

(51) Dozie Ikedife (jihar Anambra) a matsayin sakataren shiyya (Yankin kudu maso Gabas).

(52) Blessing Agbome (jihar Edo) a matsayin sakatariyar shiyya (kudu maso kudu)

(53) Lateef Ibirogba (Lagos) a matsayin sakataren shiyya (Kudu Maso yamma).

(54) John Okoho (Jihar Benue) a matsayin sakataren yada labarai na (Arewa ta Tsakiya).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.