Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya mikawa Osinbajo ragamar jagorancin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da mika ragamar jagorancin kasar ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa. Farfesa Yemi Osinbajo.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa. Farfesa Yemi Osinbajo. Présidence nigériane
Talla

Shugaban ya fadi haka neyayin ganawa da manema Labarai jim kadan kafin ya tashi daga Abuja zuwa birnin London a kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Karo na biyu kenan da shugaban Najeriyar ya mikawa mataimakin nasa ragamar jagorancin kasar, sakamakon balaguron da zai yi, tun bayan da suka hau kujerar shugabanci a shekarar 2015.

Da fari an shirya shugaban zai yi balaguron ne daga birnin Nairobi na kasar Kenya bayan ya halartar shirin kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya, amma kakakinsa Malam Garba Shehu, sanar da sauya lokacin yafiyar zuwa yau Lahadi.

Ana sa ran shugaban Najeriyar ya koma gida nan da makonni biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.