Isa ga babban shafi
Najeriya-zamfara-Ta'addanci

Bello Turji ya ce fyade ba aikinsa ba ne

Ta’addanci da satar mutane don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya.

Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji.
Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji. © Daily Trust
Talla

Kiddidiga  ta nuna cewa yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira dubu 780 a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin kasar kawai.

A wata ganawa da ya yi da jaridar ‘Aminiya’, kasurgumin dan bindigar nan mai suna Bello Turji, wanda ake zargi da yawancin ta’asar da ake aikatawa a yankin arewa maso yammacin kasar ya musanta laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Turji ya ce kowa na iya fadin abin da ya ga dama, amma abin da ya sani shine, shi ba ya fyade, yana mai cewa akwai mata a inda yake.

Ya ce da yana fyade, da ya fara da matan da ke inda yake a yanzu haka.

Turji ya bada misali da jihar Kano, inda ya ce ‘ko Bello Turji ne ya yi wa dimbim matan da aka wa fyade a Kano fyade”?

Ya ce Fulani sun dauki makamai ne don ya zame musu dole Fulani yi haka, duba da yadda aka yi ta cin zalinsu, ana sace musu shanu, kum babu wanda ya yi magana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.