Isa ga babban shafi
Najeriya - Ta'addanci

Kisan da Boko Haram ke yi a Najeriya ya ragu da kashi 72 - Rahoto

Wata sabuwar kididdiga kan ta’addanci a duniya ta nuna cewar, Najeriya ta koma matsayi na 6 a tsakanin kasashen da ke kan gaba wajen fama matsalar hare-haren na ta’addanci, cigaban da kididdigar ta alakanta da nasarar da Najeriyar ke samu a yaki da mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

A baya dai Najeriya ce ta hudu a duniya wajen fama da ta’addanci, matsayin da ta kasance a kai tun shekarar 2017.

Kididdigar da  wata cibiyar bincike kan tattalin arziki da zaman lafiya mai zaman kanta IEP ta wallafa, ta nuna cewar Najeriya, da Syria, da kuma Somalia ne kawai cikin kasashe 10 da suka fi fama da ta'addanci a duniya suka samu cigaba wajen rage girman matsalar, daga 2020 zuwa 2021.

Rahoton ya ce an samu raguwar mace-mace masu alaka da ta’addanci a Najeriya da akalla kashi 72 cikin 100, tare da danganta hakan da mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, da kuma kokarin gwamnatin kasar na fatattakar kungiyar.

Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram REUTERS/Joe Penney

A jumlace dai wannan rahoto ya nuna cewar rasa rayukan da mutane ke yi a Najeriya a dalilin ta’addanci ya ragu zuwa adadin 448 a shekarar 2021, matakin mafi karanci tun shekarar 2011.

Yawan wadanda suka mutu sakamakon ta’addancin Boko Haram ya ragu da kusan rabi a shekarar da ta gabata.

Sai dai adadin hare-haren ta'addanci ya karu da kashi 49 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021. Kashi 36 na hare-haren kungiyar ISWAP ne ke daukar alhakin kaiwa, kasha 8 cikin 100 kuma na kungiyar Boko Haram ne, yayin da kuma kashi 44, ba a danganta su da wata kungiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.