Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Majalisar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta Najeriya ta tsige mataimakin gwamnan jihar , Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau da aka tsige
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau da aka tsige © vanguard
Talla

A wani zaman farko da ‘yan Majalisar suka yi a wannan Laraba, mambobi 20 daga cikin 24 sun kada kuri’ar amincewa da tsige mataimakin gwamnan bayan wani rahoto da kwamitin bincike na majalisar ya same shi da aikata wasu laifuka.

An zargi Gusau da yin amfani da karfin kujerarsa wajen aikata laifukan kamar yadda kwamitin binciken ya bayyana a cikin rahotonsa wanda aka mika wa shugaban Majalisar Dokokin Hon. Nasiru Mu’azu Magarya a yau Laraba.

Shugaban Majalisar ne ya karanta bayanan da ke kunshe cikin rahoton a zauren Majalisar Dokokin.

Gusau dai ya sha korafin cewa, yana fuskantar musgunawa daga gwamnan jihar, Bello Mutawalle sakamakon banbancin jam’iyya.

Tun bayan da gwamna Mutawalle ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC daga PDP, Gusau ya ki biye masa, yana mai cewa, yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, abin da wasu ke kallo a matsayin musabbabin bita-da kulli a gare shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.