Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan majalisun PDP sun bukaci Buhari ya yi watsi da Gwamnoni kan doakar zabe

‘Yan Majalisar dokokin Najeriya da suka fito daga Jam’iyyar PDP sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi watsi da korafin Gwamnonin kasar wajen rattaba hannu akan sabuwar dokar zaben da aka yiwa gyaran fuska.

Tutar jam'iyyar adawar Najeriya PDP
Tutar jam'iyyar adawar Najeriya PDP vanguardngr
Talla

Yayin ganawa da shugabannin gudanarwar Jam’iyyar su a Abuja, ‘Yan Majalisun sun yi zargin cewar Gwamnonin APC na rokon shugaban da yaki sanya hannu akan dokar wadda jama’ar kasa ke fatar ganin ta fara aiki.

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Ndidi Elumelu ya roki shugaban ya sanya hannu akan dokar domin karfafa dimokiradiya da kuma barin tarihi inganta harkokin zaben kasar.

Takaddama tsakanin Majalisar dokoki da Gwamnonin kasar ta barke lokacin da Majalisar ta amince da sabuwar dokar zabe wadda zata baiwa jama’a amfani da tsarin kato bayan kato wajen tsayar da Yan takarar zaben kujeru daban daban.

Rahotanni sun ce matsin lamba daga gwamnonin ya sanya shugaban kasa kin sanya hannu akan dokar, abinda ya sa majalisar ta sake mata gyarar fuska, ta kuma mayar masa a jiya litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.