Isa ga babban shafi

Babu labarin dalibai mata 110 da Boko haram suka sace a Sakandaren Chibok

Al'umomin jihar Barno dake Najeriya sun ce har ya zuwa yanzu babu labarin dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan boko haram suka sace a Sakandaren Chibok a shekarar 2014.

Wasu daga cikin daliban Chibok da aka sako  a baya.
Wasu daga cikin daliban Chibok da aka sako a baya. AFP/File
Talla

Wata kungiyar da ake kira Kibaku ta raya Yankin Chibok, wadda ke sahun gaba wajen fafutukar ganin an ceto Yam matan ta hannun shugaban ta Dauda Iliya tace daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar gudu daga hannun wadanda akayi garkuwa da su.

Taswirar Najeriya
Taswirar Najeriya Sophie RAMIS AFP

Iliya yace daga shekarar 2012 zuwa yanzu an kashe mutane sama da 72 a yankin, yayin da aka sace sama da 407, tare da kona gidaje da wuraren sana’oi da mujami’u da kayan abinci da kuma  sace motoci sama da 20.

Wasu daga cikin kungiyoyin dake fafutukar ganin an sako daliban Chibok
Wasu daga cikin kungiyoyin dake fafutukar ganin an sako daliban Chibok REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban al’ummar yace daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu, mayakan book haram sun zafafa hare haren su a yankin, ciki harda wanda aka kai kautikari a ranar 14 ga wannan wata inda aka sace Yam mata 5 tare da kasha mutane 3 da kuma kona gidaje da mujami’u.

Jami’in yace har yanzu suna jiran hukumomin Najeriya su ceto musu dalibai mata 110 da aka sace a shekarar 2014, tare da bukatar kara yawan sojoji da kayan aiki a Chibok domin dakile hare haren da ake kai musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.