Isa ga babban shafi
Najeriya - Kano

Buhari ya ba da umarnin tabbatar da bin hakkin yarinyar da malaminta ya kashe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci hukumomin ‘yan sanda da na ma’aikatar shari’a da su tabbatar yin adalci wajen aiwatar da hukunci kan kisan da aka yi wa Hanifa Abubakar, daliba ‘yar shekara biyar a jihar Kano.

AbdulMalik Muhammad Tanko malamin makarantar da ya kashe dalibarsa Hanifa Abubakar mai shekaru 5
AbdulMalik Muhammad Tanko malamin makarantar da ya kashe dalibarsa Hanifa Abubakar mai shekaru 5 © Daily Trust
Talla

Buhari ya ba da umarnin ne a jiya Juma’a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar, dangane da mutuwar Hanifa da aka yi garkuwa da ita tun a cikin watan Disambar shekarar bara.

Shugaban ya jajantawa iyaye da ‘yan uwan dalibar da aka gano gawarta a wani kabari mara zurfi a Kano bayan an shafe kusan watanni biyu ana bincike.

Hanifa Abubakar, dalibar da malaminta ya yiwa kisan rashin imani a jihar Kano.
Hanifa Abubakar, dalibar da malaminta ya yiwa kisan rashin imani a jihar Kano. © Daily Trust

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe makaranta mai zaman kanta, ‘Noble Kids Academy’ da ke karamar hukumar Nassarawa, inda aka gano gawar daliba Hanifa Abubakar da malaminta mai suna AbdulMalik Muhammad Tanko ya kashe.

Yayin gudanar da bincike kan isan rashin imanin, Abdulmalik ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsa akai, inda ya ce, bayan sace Hanifa, ya kaita gidansa inda ya tuntubi ‘yan uwanta kan su biya Naira Miliyan Shida a matsayin kudin fansa.

Daga bisani ne kuma bayan lura da cewar yarinyar ta gane shi ne, malamin ya yanke shawarar shayar da dalibar tasa guba, tare da binne gawarta da ya sassara a wani kabari mara zurfi da yah aka harabar makarantar Noble Kids Academy da ke karamar hukumar Nasarawa.

Yanzu haka dai dubub dubatar mutane a ciki da wajen Najeriya, na cigaba da yin Allah wadai da kisan rashin imanin da AbdulMalik Tanko ya yi wa dalibarsa, inda jama'a ke kiraye-kirayen gaggauta hukunta shi daidai da abinda ya aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.