Isa ga babban shafi
Zamfara-MDD

MDD ta nuna damuwa kan kisan kiyashin Zamfara

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki kisan kiyashin da aka yi wa mutane a jihar Zamfara ta Najeriya a makon jiya, yayin da ya bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta hukunta miyagun da suka aikata wannan laifin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ANWAR AMRO AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan bindiga karkashin jagorancin Bello Turji sun kai farmaki kan wasu kauyuka biyar tare da kona gidajen al’umma kurmus a cikin kwanaki biyu da suka shafe suna cin karensu babu babbaka.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar, Antonio Guterres ya mika sakon jaje da ta’aziya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a harin na ‘yan bidigar.

Ya kara bada tabbacin cewa, Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya a yakin da take yi da matsalar tsaro, amma ya roki gwamnatin kasar da ta matsa kaimi domin hukunta masu hannu a kisan kiyashin na Zamfara.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi tur da harin tare da fadin cewa, gwamnatinsa za ta yi amfani da dukaknin karfinta wajen murkuse ‘yan bindigar har su zama tarihi.

Kauyukan da ‘yan bindigar suka yi wa ta’adi a makon jiya, sun hada da Tungar Geza da Rafin Gero da Kurfar Danya da Kewaye da kuma Tungar Na More.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.