Kashe 'yan bindiga shi ya fi dacewa da su - El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya Nasir El-Rufa’I ya hakikance cewa dole ne a kashe ‘yan bindigar da ke addabar al’umma domin kuwa bai amince da zancen yi musu afuwa ko kuma gyaran halayyarsu ba.
Wallafawa ranar:
Gwamnan ya ce, hanya mafi dacewa wajen hulda da ‘yan bindigar da sauran ‘yan ta’adda da ke haddasa rashin tsaro a kasar, ita ce a aika su lahira.
Gwamnan ya bayyana matsayarsa ce a yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a jiya Talata jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari.
EL-Rufa’I ya ziyarci shugaban kasar domin yi masa bita kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan jama’a a baya-bayan nan a Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.
Ba a karon farko ba kenan da gwamnan ya sha bayyana cewa, bai dace a yi sulhu da wadannan mutane masu kisan jama'a ba gaira ba dalili ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu