Isa ga babban shafi
Najeriya-Sokoto

'Yan bindiga sun kona matafiya 42 da ke hanyar zuwa ci rani a Sokoto

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun kona matafiya 'yan cirani 42 a cikin motar su a kauyen Gidan Bawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto, kuma ana fargabar cewar akasarin su sun mutu.

'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya musamman jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina da kuma jihar Neja.
'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya musamman jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina da kuma jihar Neja. News Agency of Nigeria (NAN)
Talla

Bayanai daga yankin sun ce matafiyan na kan hanyar su ce ta zuwa Gadar Gayan domin tafiya kudancin Najeriya lokacin da suka fada hannun ‘yan bindigar.

Shaidu daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun bude wuta akan motar ce, inda suka fasa tayun ta, abinda ya kai ga faduwar ta da kuma kamawa da wuta.

Wani ‘dan sakai ya ce fasinjojin sun kunshi mazauna yankin da wasu da suka fito daga Jamhuriyar Nijar.

‘Dan majalisar dokokin jihar Sokoto Ibrahim Sa'idu ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Jaridar Daily Trust, inda ya ce ‘yan bindigar na ci gaba da kwace babura da wayoyi da kuma wasu kadarori da gonaki.

Ibrahim Sa'idu ya kuma ce 'yan bindigar sun kwashe mutane 9 daga kauyen Masawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.