Isa ga babban shafi
NAJERIA-SARAUTA

Daruruwan mutane suka halarci jana'izar Sarkin Ban Kano Mukhtar Adnan

Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar Sarkin Ban Kano kuma Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtar Adnan, wanda ya rasu yau yana da shekaru 95 a duniya.

Sarkin Ban Kano, Alhaji Mukhtar Adnan
Sarkin Ban Kano, Alhaji Mukhtar Adnan © Daily Trust
Talla

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu da Alhaji Aminu Dantata da Tsohon Gwamnan Kano Engr Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun ce Alhaji Adnan ya rasu ne yau yana da shekaru 95 a duniya, bayan ya kwashe shekaru 63 a karagar Hakimcin Dambatta wanda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na farko ya nada shi a shekarar 1954 domin gadon mahaifin sa.

Sarkin Kano Ado Bayero na daya daga cikin wadanda Sarkin Ban Kano ya shiga cikin wadanda suka zabe su domin hawa karagar Masarautar Kano
Sarkin Kano Ado Bayero na daya daga cikin wadanda Sarkin Ban Kano ya shiga cikin wadanda suka zabe su domin hawa karagar Masarautar Kano REUTERS/Stringer

An dai haifi Sarkin Ban ne a shekarar 1926, kuma yayi karatu a Makarantar Elementary dake Dambatta da Makarantar Sakandaren Kano Middle School, kafin ya wuce zuwa Zaria inda inda ya samu horo a matsayin Akawu.

Alhaji Adnan yayi aiki da karamar hukumar Kano ta wancan lokaci da ake kira NA inda ya rike mukamai daban daban kafin daga bisani a nada shi a matsayin Sarkin Bai.

Lokacin Jamhuriya ta farko a siyasar Najeriya, Alhaji Adnan na daga cikin ‘Yan majalisun tarayya daga Jihar Kano, yayin da a shekarar 1968 ya zama kwamishinan ilimi.

Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi na II
Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi na II REUTERS/Joe Penney

Rahotanni sun bayyana Sarkin Ban a matsayin Dan Majalisar Sarkin Kano da ya fi dadewa a karaga tun bayan kafa ta a karni na 19, ganin yadda ya kwashe shekaru 63 a matsayin Hakimi da ‘Dan Majalisar Sarki kana kuma mai zaben Sarki.

Alh Adnan na daga cikin masu zaben Sarkin da suka zabi Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a shekarar 1963 da Ado Bayero a shekarar 1963 da Muhammadu Sanusi na Biyu a shekarar 2014 da kuma Aminu Ado Bayero a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.