Isa ga babban shafi
Najeriya-UNICEF

'Yan Najeriya miliyan 46 na bahaya a bainar jama'a- UNICEF

Asusun UNICEF ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta farko a duniya da ke fama da matsalar yin bayan gida a bainar jama’a.

Wasu 'yan Najeriya.
Wasu 'yan Najeriya. STRINGER / AFP
Talla

Jami’in hukumar Sam Adejo Okedi ya ce duk da ci gaban da aka samu ‘yan Najeriya miliyan 46 ke bayan gida a fili, matakin da ke barazana ga lafiyar jama’a.

Alkaluman hukumar da aka gabatar na kananan hukumomin Najeriya 774 sun nuna cewar a kananan hukumomi 10 ne kacal ba a samun masu bayan gida a fili, wanda shi ne kashi 10 bisa 100 a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar anyi nasarar magance matsalar da ake samu na yawaitar masu bayan gari a bainar jama’ar a Jihohin Jigawa da Katsina da kuma Benue.

Shugaban hukumar UNICEF da ke kula da shiyyar Kano da Sokoto Maulid Warfa ya bayyana haka, inda ya danganta ci gaban da matakin da hukumomin yankunan ke dauka na magance matsalar.

Warfa yace an samu nasarar dakile wannan dabi’ar ce a kananan hukumomi 21 dake Katsina da 18 dake Jigawa da kuma guda 9 dake Benue.

Jami’in yace kashi 25 na mutanen dake zama a yankin arewa maso yammacin Najeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su, yayin da kashi 35 kuma ke samun kula ta fannin tsafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.