Isa ga babban shafi
Lagos-EndSARS

Masu bincike sun gabatar da rahoton tarzomar EndSARS a Lagos

A Najeriya, kwamatin bincike a game da zargin kisa da kuma azabtarwa da ake yi wa jami’an tsaro lokacin tarzomar EndSARS da aka yi a bara, ya gabatar da rahotonsa ga gwamnatin jihar Lagos.

Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS.
Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A shekarar da ta gabata ne wani gungun matasa ciki har da mawaka da masu fafutukar kare hakkin bil adama, ya kaddamar da boren EndSARS, da nufin kawo karshen cin zarafi, aikata kisa da kuma zargin tatsar kudade daga hannayen jama’a da ake yi wa ‘yan sandan kasar.

Wannan dai bore ne da ya mamaye birane da dama a kasar kafin ranar 20 ga watan Oktoban bara lokacin da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi don kawo karshensa ta hanyar bude wuta a kan masu tarzoma daf da wurin binciken ababan hawa da ake kira Lekki Tollgate a Lagos.

Tun a wancan lokaci kungiyoyin kare hakkin dan adam har da Amnesty International sun yi zargin cewa an kashe mutane akalla 10 ta hanyar harbin su da bindiga, zatgin da gwamnatin Najeriya ta musanta.

Kwanaki kadan bayan faruwar lamarin ne gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya kafa kwamitin musamman don binciken wannan zargi, kuma shugaban kwamitin mai shara’a Doris Okuwobi, wanda ya gabatar da rahoton a ranr Litinin, ya ce sun yi la’akari da korafe-korafe 186 daga cikin 252 da aka gabatar masu kafin kammala rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.