Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane shida a wani hari a Katsina

‘Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan al’ummar Katsina yayin da aka kashe mutane shida a kauyen Gwarjo da ke yankin karamar hukumar Matazu, da daren ranar Juma’ar da ta wuce a

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI
Talla

Mazauna yankin sun ce harin ya kuma jikkata mutum tara.

Bayanan da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta tattara, sun ce maharan sun isa kauyen da misalin karfe tara na dare, inda suka dauki tsawon sa’o’i hudu su na harbin kan mai ‘uwa dawabi, kafin su fice.

Yanzu haka dai mutane da dama ne ba a san inda suke ba, amma dai akwai yakinin cewa ba garkuwa da su maharan suka yi ba. Ko da yake rahotanni sun fi karkata ne kan cewa da dama sun tsere cikin daji ne sakamakon fargaba.

Haka zalika Jaridar ta Premium Times ta ruwaito cewa muharan sun yi awun gaba da babura hudu na mazauna kauyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.