Ma'aikatan jiragen kasa za su fara yajin aikin gargadi na kwanaki 3
Ma'aikatan sufurin jiragen kasa a Najeriya za su shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3 daga ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba zuwa 20 ga Nuwamba.
Wallafawa ranar:
Babban sakataren kungiyar ma'aikatan layin dogo a Najeriya (NUR), Kwamared Segun Esan, ya tabbatar da haka, kuma rahotanni na cewa tuni kungiyar ta sanar da mahukunta Shirin shiga yajin aikin.
A baya dai kungiyar masu aikin jiragen kasa ta Najeriya NUR da ‘yar uwarta, ta manyan ma’aikatan hukumar da kuma kamfanin na gwamnati, sun baiwa gwamnatin tarayya da hukumar kula da jiragen kasa ta kasa wa’adin makonni uku don biyan wasu bukatunsu da suka hada da karin albashi da alawus- alawus daga ranar 14 ga watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu