Shugaban Najeriya zai halarci taron yanayi na COP 26
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron sauyin yanayin da aka yiwa lakabi da COP26 a Glasgow dake Scotland, inda zai gabatar da irin matakan da kasar ke dauka wajen yaki da sauyin yanayi.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya rabawa manema labarai tace shugaban zai yiwa taron jawabi a ranar talata, yayin da kuma zai halarci wasu tarurruka da shugaban Amurka Joe Biden da shugaban Faransa Emmanuel Macron zasu jagoran ta.
Shehu ya kuma ce Buhari zai jagoranci taron ‘Yan kasuwa da masu zuba jari daga Najeriya da Faransa wanda zai gudana a birnin Paris inda ake saran halartar wakilan gwamnatocin kasashen biyu da yan kasuwa da jami’an diflomasiya da kuma Yan jaridu.
Sanarwar tace ziyarar Buhari Paris zata kuma bashi damar halartar taron zaman lafiya karo na 4 da shugaba Emmanuel Macron zai jagoran ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu