Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Fasinjojin jirgin kasa sun tsallake rijiya da baya tsakanin Kaduna da Abuja

Wasu fasinjojin dake tafiya ta jirgin kasa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja dake Najeriya sun tsallake rijiya da baya sakamakon harin da ake zargin ‘yan bindiga sun kai musu wajen amfani da na’urorin dake fashewa tare da bindigogi akan jirgin da suke ciki a yammacin laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © John Angelillo / Pool / REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce a harin na jiya direban jirgin yayi nasarar janye shi inda ya mayar da shi Kaduna inda ya fito ba tare da wani ya jikkata ba, sai dai gaban jirgin ya lalace sakamakon harin.

Sanata Shehu Sani, na daya daga cikin wadanda ke cikin jirgin yau da safe, lokacin da ya sake taka wani abu mai kama da nakiya, kafin yayi sa’ar wucewa.

Wasu daga cikin jiragen da gwamnatin Buhari ta kaddamar
Wasu daga cikin jiragen da gwamnatin Buhari ta kaddamar STRINGER / AFP

A tattaunawar da yayi da RFI Hausa tsohon Dan Majalisar Dattawan ya bayyana harin a matsayin tashin hankali, wanda ya jefa fasinjojin jirgin cikin mawuyacin hali kafin su kubuta.

Shugaban Hukumar kula da sufurin jiragen kasar Najeriya Fidet Okhiria ya tabbatar da samun matsalar amma yace ya zuwa wannan lokaci ba zasu iya cewa ‘Yan ta’adda ne suka kai harin ba, har sai abinda bincike ya nuna.

Fidet ya danganta matsalar da aka samu da bata gari da kan kai hari akan layin dogon a hirar da yayi da Jaridar Daily Trust.

Shugaban Hukumar yace suna iya bakin kokarin su wajen gyara hanyar da ta baci, kuma da zaran sun kamala sufurin jiragen zai ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.