Isa ga babban shafi
Zamfara-'Yan bindiga

'Yan sanda sun kubutar da mutane kusan 200 daga 'yan bindiga a Zamfara

Jami'an saro a Najeriya sun yi nasarar ceto akalla mutane 200 da a kayi garkuwa da su a jihar Zamfara bayan sun kwashe dogon lokaci a hannun 'yan bindiga.

Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara.
Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara. AP - Ibrahim Mansur
Talla

'Yan sanda a jihar Zamfarar sun ce, mutane 187 jami’ansu suka kubutar da suka hada da maza da mata da kuma yara kanana.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Mohammed Shehu ya ce wasu daga cikin wadanda aka kubutar sun kwashe dogon lokaci a hannun 'yan bindigar wadanda ke jiran karbar diyya kafin su sake su.

'Yan sandan sun nuna hoton mutanen da suka ceto zaune a kasa cikin matsatsi bayan nasarar kubutar da su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaron kasar ke sanar da samun nasara akan 'yan bindigar da suka addadi yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kai hare-hare kan kauyuka tare da sace jama'a domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.