Najeriya-Kaduna
Al'ummar Kaduna sun kalubalanci matakan gwamnati na yaki da 'yan bindiga
Al'umma da dama a jihar Kaduna da ke Najeriya na kokawa dangane da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na dakile aikin 'Yan ta'adda a jihar inda su ke ganin cewa matakan sunyi tsauri da yawa, kuma suke bukatar a sassauta. A makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta hana hawa babura a fadin jihar har na tsawon watanni uku tare kuma katse layukan sadarwa a wasu sassan jihar. Wakilinmu daga Kaduna Aminu Sani Sado na dauke da rahoto akai.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:03