Isa ga babban shafi
Najeriya -CBN

Babu shirin mayar da asusun ajiyar kudaden kasashen waje zuwa na Naira - CBN

Babban bankin Najeriya ya musanta ikirarin da ake cewa ya  umurci bankuna su mayar da asusun ajiyar abokan huldarsu  na kudaden kasasehn waje zuwa na Naira.

Takardar kudin Najeriya na Naira.
Takardar kudin Najeriya na Naira. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A wata sanarwa ta ya fitara a Asabar, daraktan yada labaran bankinOsita Nwanisobi, ya ce babu gaskiya a wannan  ikirarin, hasali ma sanarwar da ake ta yadawa a game da haka karya ce tsagwararta.

Bankin ya sake yin tuni da cewa ya sha bada tabbacin cewa babu wani shirn mayar da asusun ajiyar kudaden kasashen waje zuwa na Naira, don kawai yana so ya magance karancin dalar Amurka.

Daga nan sai banki ya ja kunnen kamfanoni da daidaikun mutane a game da amfani da hatimi ko alamar bankin, yana mai cewa ya sanar da hukumomi, kuma duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.