Isa ga babban shafi
Katsina

Cutar Kwalara ta kashe mutane fiye da 150 a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya, ta ce zuwa yanzu mutane sama da 150 aka tabbatar mutuwarsu daga cikin wasu akalla dubu 5 da 677 da suka kamu da cutar Kwalara, tun bayan barkewar a jihar kimanin wata guda da ya gabata.

Hoton na'urar Komfuta da ke nuna kwayoyin da ke haddasa cutar Kwalara.
Hoton na'urar Komfuta da ke nuna kwayoyin da ke haddasa cutar Kwalara. Fuente: Wikipedia.
Talla

Babban Sakataren Hukumar Kula da Kula da Lafiya a matakin Farko a Katsina, Dakta Shamsudeen Yahaya, ya shaidawa manema labarai cewa, an tattara alkaluman ne daga asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da ke jihar.

Jami’in ya kuma bayyana fargabar adadin wadanda suka mutu na iya zarta wanda aka kididdige, kasancewar akwai mutane da dama musamman a karkara, da ba sa zuwa asibiti.

A farkon watan Agusta hukumomin jihohin Sokoto da Zamfara suka sanar da mutuwar mutanen da yawansu ya kai 53, 30 daga cikin su Zamfara, yayin da 23 suka mutu a Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.