Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari zai sallami wasu karin ministocinsa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, akwai yiwuwar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sake sallamar wasu daga cikin ministocinsa sakamakon rashin taka rawar gani.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Wata majiyar sirri daga fadar shugaban kasa ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, nan gaba kadan akwai karin ministocin da shugaba Buhari zai sallama.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya tube Alhaji Sabo Nanono daga kujerar Ministan Noma da kuma takwaransa na Wutar Lantarki Engr Sale Mamman.

A karon farko kenan da shugaba Buhari ke daukar tsattsauran mataki na tube wasu daga cikin ministocinsa tun bayan da ya dare kujerar shugabancin Najeriya a 2015.

Buhari ya maido da akasarin ministocin da ya yi aiki da su a lokacin wa’adin mulkinsa na farko bayan da ‘yan Najeriya suka sake zaben sa a 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.