Isa ga babban shafi
DOKAR-HANA YAWON KIWO

Alkalami ya bushe dangane da hana kiwo a kudancin Najeriya - Akeredolu

Gwamnan Jihar Ondo dake Najeriya Rotimi Akeredolu ya bayyana cewar alkalami ya bushe dangane da dokar da gwamnonin kasar suka amince da ita ta hana yawon kiwo, wadda zata fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, kuma duk wanda aka samu yana yawon kiwon zai fuskanci hukunci.

Shugaban gwamnonin kudancin Najeriya Rotimi Akeredolu
Shugaban gwamnonin kudancin Najeriya Rotimi Akeredolu Twitter/@RotimiAkeredolu
Talla

Akeredolu dake shugabancin gwamnonin kudancin Najeriya 17 ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da sabon mataimakin Sufeto Janar na Yan Sandan kasar Ene Okon da ya ziyarce shi a birnin Akure.

Gwamnan yace sun dauki matakin hana yawon kiwon ne domin kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya, yayin da ya kare matakin kafa rundunar tsaro ta Amotekun wanda yace an kafa ta ne domin taimakawa wajen samar da zaman lafiya amma ba domin yin gasa da hukumomin tsaron kasa ba.

Shanun da dokar hana yawon kiwo zata shafa
Shanun da dokar hana yawon kiwo zata shafa Daily Trust

Akeredolu yace doka akayi amfani da ita wajen kafa rundunar domin tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma, ganin yadda ake samun raguwar jami’an tsaro da kuma karuwar aikata laifuffuka.

Sabon mataimakin sufeto Janar din, Ene Okon ya yabawa gwamnan saboda jajircewar sa wajen kafa rundunar Amotekun domin samar da tsaro.

Okon yace yana da masaniyar jihar Ondo na daya daga cikin jihohin dake fuskantar rikicin manoma da makiyaya, amma yanzu labarin ya sauya saboda zaman lafiyar da aka samu, abinda ya rage nauyin dake kan jami’an Yan Sanda da kuma sauran hukumomin tsaron dake aiki a jihar.

Okon yace yayi ta karanta irin sukar da wasu mutane ke yiwa rundunar Amotekun da kuma jajircewar Akeredolu wajen samar da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.