'Yan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici a tsakaninsu
Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta ce ‘yan bindiga 9 ne suka mutu sakamakon wani kazamin rikici da ya barke a tsakaninsu a wani kauye da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.
Wallafawa ranar:
Samuel Aruwan, wanda shine kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa wani kasurgumin dan bindiga da ake wa inkiya da Godon Mota ne ya kutsa da shi da tawagarsa kauyen Garke a Larabar da ta gabata, kuma nan ne rikici tsakanin abokan hamayyar ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 9.
Aruwan ya ce har yanzu ba a tantance ummul’aba’isin rikicin nasu ba, amma ana zargin ba zai rasa nasaba da rabon kudin fansa da suka tara ba.
Jihar kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da ayyukan ‘yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu