Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

Masu satar mutane a babban birnin Tarayyar Najeriya sun fara ta’asarsu gabagadi, inda suke ci gaba da nuna rashin tsoro, don yanzu sun fara karbar kudin fansa ta asusun banki, akasin yadda suka saba.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

A makon da ya gabata kawai ‘yan bindiga sun yi satar mutane har sau biyu a unguwar Tungan Maje, dake wajen birnin Tarayyar Najeriya, Abuja. Maharan sun sake komawa unguwar a aranar Laraba, bayan da suka sace mutane 6 a wurin tun da farko.

Sauran garuruwan kewaye da Abuja kamar su Kuje, Bwari, Abaji sun fuskanci tsanantar ayyukan masu satar mutane a ‘yan watannin da suka gabata.

A yayin da wadannan masu satar mutane kan saki wadanda suka kama bayan an biya kudin fansa a hannu, yanzu wani sabon salo suka bullo da shi na karbar kudin fansa ta asusun banki.

A watan Afrilun da ya gabata, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Kingsley Mogalu ya yi zargin cewa masu satar mutane da ‘yan ta’adda sun fara neman a biya su da kudin intanet na cryptocurrency, inda ya nemi hukuma ta bullo da matakan dakile su.

Wasu iyalai sun bayyana yadda masu satar mutane suka tilasta musu biyan kudin fansa ta banki, bayan da suka sace musu ‘yan uwa a garin Madalla.

Mr. Adewuyi, da aka yi garkuwa da matarsa ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa Najeriya cewa ‘yan bidiga sun san umurce shi ya biya kudin fansar maidakinsa ta asusun bankin Access mai lamba: 1403762272 da suna: Badawi Abba. Adewuyi ya ce ya kai rahoton al’amarin ga ofishin ‘yan sanda dake Jabi Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.