Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara-'Yan bindiga

‘Yan bindiga sun yi wa garin Dansadau dirar mikiya

‘Yan bindiga da ba a san adadinsu ba sun kai farmaki  garin Dansadau da ke karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfara a Najeriya.

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI
Talla

Rahotanni daga garin na Dansadau na cewa da misalin karfe 2 da rabi na asubahin Juma’ar nan ne ‘yan bindigar suka shiga garin, inda aka yi ta fama da su har zuwa karfe 5 da rabi na safiya, lamarin da ya sa ko sallar asuba babu wanda ya samu sukunin yi.

Wani mazaunin garin, wanda ganau ne ba jiyau ba, Nuhu Dansadau, ya shaida wa sashen Hausa na RFI cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 15, cikin su akwai matan aure 8, yara 4 da magidanta 3.

Sun kuma kashe mutane 4, wadanda da safiyar Juma’ar nan aka yi yi jana’izar su.

Ya  ce tinkarar ‘yan bindigar da al’ummar gari da sojoji suka yi ne ma ya takaita barnar da ‘yan bindigar suka kitsa musu.

Akwai hasashen cewa wannan hari da aka kai wa al’ummar garin Dansadau, yana da nasaba da taimaka wa matukin jirgin saman yakin sojin Najeriya da suka yi ne bayan da ‘yan bindiga suka harbo jirginsa, ya rikito, wanda bayan haka ‘yan bindigar suka sha alwashin cewa ba mai yin bikin Sallah lafiya a garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.