Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SUFURI

Yan Najeriya 350 suka mutu a hadarin jiragen ruwa - HYPPARDEC

Hukumomin Najeriya sun ce akalla mutane 350 suka mutu sakamakon hadurran kwale kwale da aka samu a cikin kasar a shekarar 2020, abinda ke nuna yadda ake samun karuwar hadura a sufurin jiragen ruwa a kasar.

Wani bangare na kogin Neja da Benue a Najeriya.
Wani bangare na kogin Neja da Benue a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Shugaban majalisar gudanarwar Hukumar HYPPARDEC dake kula da yankunan dake samar da wutar lantarki Joseph Ityav ya bayyana haka a Borgu dake Jihar Niger.

Ityav wanda ya ziyarci Malale dake karamar Hukumar Borgu domin kaddamar da shirin sare itatuwa da kuma dattin da suka mamaye kogin Kainji da Shiroro ya danganta hadurran da rashin ingancin kwale kwalen da ake amfani da su da dibar mutanen da suka wuce kima da kuma rashin amfani da rigar dake hana mutane nitsewa a cikin ruwa sai kuma itatuwan dake tare hanyar da kwale kwalen ke bi.

Shugaban majalisar yace sare itatuwa da kuma kwashe sharar dake tare hanyoyin da kwale kwale ke bi zai taimaka wajen rage wahalar da mutanen dake zama a kusa da bakin ruwa ke fuskanta.

Daraktan Hukumar HYPPARDEC Abubakar Yelwa yace za suyi iya bakin kokarin su wajen shawo kan matsalolin dake haifar da hadura a Kainji da Shiroro.

A shekarar 1964 gwamnatin Najeriya ta gina madatsaruwan Kainji akan kogin Naija akan kudi dala miliyan 209 kuma aka fara aiki da shi a shekarar 1968, yayin da aka gina madatsar ruwan Shiroro a shekarar 1983.

A ranar 27 ga watan Mayu kwale kwalen dake dauke da mutane 160 ya kife a Warrah dake Jihar Niger inda aka tsamo gawarwaki 97, sauran mutanen kuma suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.