Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Zulum ya sha alawashin taimakawa manoman jiharsa

Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum yau ya ziyarci garin Damasak dake kusa da Tafkin Chadi domin karfafawa mutanen yankin ci gaba da gudanar da aikin noma a daidai lokacin da damina ta fara zama a yankin.

Gwamna Zulum a gonar shinkafa Damasak
Gwamna Zulum a gonar shinkafa Damasak © Borno Government
Talla

Yayin ziyarar Zulum ya bada umurnin tattara bayanan iyalai 3,000 da za’a baiwa tallafin kayan aikin noma da suka hada da ingantaccen iri da takin zamani da injin din ban ruwa da kuma maganin kashe kwari domin ganin sun koma gonakin su da taimakon jami’an sojin Najeriya.

Mai magana da yawun Gwamnan Isa Gusau yace wannan shine karo na 2 da iyalai 3,000 zasu ci gajiyar irin wannan shirin na samun tallafin kayan noman rani da na damina, kuma an shirya kowanne iyali guda na dauke da mutane akalla 6 abinda ke nuna cewar mutane 18,000 zasu amfana da shirin.

Wasu manoman shinkafa dake aikin girbi a Damasak
Wasu manoman shinkafa dake aikin girbi a Damasak © Borno Government

A watan Janairun da ya gabata, Gwamnan da ya ziyarci Damasak ya sanya ido wajen raba iri da takin zamani da maganin kashe kwari da injin din ban ruwa da kuma naira N5,000 ga manoma 1,200 wadanda yanzu haka ke girbe amfanin gonakin su da suka hada da albasa da shinkafa da kuma tattasai.

Yayin ziyarar sa ta yau, Gwamna Zulum ya zagaya wasu daga cikin gonakin dake yankin domin ganewa idan sa halin da ake ciki inda ya bayyana gamsuwar sa da irin ci gaban da aka samu.

Aikin girbin shinkafa
Aikin girbin shinkafa © Borno Government

Gwamnan ya sha alwashin ci gaba da tallafawa manoman domin ganin sun ci gaba da ayyuka a gonakin su bayan kwashe shekaru 6 ba’a aikin noma saboda rikicin boko haram da ya addabi yankin a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.