Isa ga babban shafi
Najeriya - Talauci

Karin 'Yan Najeriya miliyan 7 na fama da talauci - Bankin Duniya

Kwana uku bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 daga kangin talauci, Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin kayayyakin abinci ya sa mutane miliyan bakwai cikin talauci.

Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa
Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa © Rfi hausa / Ahmed Abba
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce hauhawar farashin ya sauka da kashi 0.19 cikin 100 a cikin watan Mayu na wannan shekarar 2021, yayin da ake ci gaba da korafi a tsakanin ’yan Najeriya kan tsadar bukatun yau da kullum kamar abinci da magunguna da sauran kayayyakin masarufi..

Masana sun ce rahotan Bankin Duniya bai ba su mamaki ba, idan aka yi la’akari da cewa hatta hukumar kididdiga ta gwamnatin kasar NBS ta sha yin bayyanan hauhawan farashi a watannin da suka gabata dangane da ya sanya tsadar kayayyakin masarufi.

A cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce: “Farashin abinci ya kai sama da kashi 60% na jimillar karuwar hauhawar farashin kaya''.

Wanda yayi sanadaiyar sanya ‘yan Najeriya kimamin miliyan 7 cikin kangin talauci a shekarar 2020 da ta gabata.

Sanarwar da mai magana da yawun bankin, Mansir Nasir ya sanya wa hannu ta ce yayin da gwamnati ke daukar matakan kare tattalin arzikin daga shiga masassara, yana da muhimmanci a tsara manufofi masu inganci don murmurewa.

Masanin tattalin arziki Dr Isa Abdullahi na Jami'ar Kashere ya danganta hauhawan farashin da matsalar da aka samu wajen aikin noma sakamakon yadda rikice rikice da hare haren Yan bindiga suka hana manoma zuwa gonakin su da kuma matsalar ambaliya da sauyin yanayi.

Masanin yace yayin da wasu daga cikin wadannan matsaloli mutane ne ke haifar da su, ya dace hukumomi su tashi tsaye wajen samar da tsaron da manoma zasu koma gonakin su domin samar da abinci da kuma rage dogaro da shigar da shi daga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.