Isa ga babban shafi
Najeriya

Dattawan arewacin Najeriya sun mayar da martani ga Gwamnonin Kudu

Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta zargi Gwamnonin da suka fito daga yankin kudancin kasar da gina mutanen dake da tsananin nuna kabilanci da kuma buya a bayan su suna tinzira jama’a domin rabakan jama’ar kasa.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin ganawa da takwaransa na Afirka ta Kudu a Pretoria, 3 ga watan Oktoban 2019
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin ganawa da takwaransa na Afirka ta Kudu a Pretoria, 3 ga watan Oktoban 2019 REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Sanarwar da kungiyar ta gabatar mai dauke da sanya hannun kakakin ta Dr Hakeem Baba Ahmed ta zargi gwamnonin da suka yi rantsuwar kare kundin tsarin mulki da bada kai ga masu fafutukar raba kann kasa.

Ahmed ya bayyana matakin da gwamnonin kudancin kasar suka dauka na hana yawon kiwo a matsayin wani yunkuri raba kann arewacin kasar.

Sanarwar tace yanzu ya bayyana karara cewar zababbun wakilan da suka yi rantsuwar kare kundin tsarin mulki da cigaba da dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sun gaza wajen aiwatar da nauyin da ya rataya akan su.

Bukatar raba kasa

Dattawan arewacin Najeriyar sun ce a Yankin Kudu maso Gabas gwamnonin sun bada kai ga masu fafutukar ballewa daga kasar da masu aikata laifuffuka da suke tunanin murkushe hukumomin gwamnatin tarayya da kuma yan arewa dake yankin domin cimma burin su na siyasa a shekara mai zuwa.

Sanarwar tace a yankin kudu maso yamma kuma, zababbun yan siyasar na taimakawa masu fafutukar nuna banbancin kabilanci domin neman ganin an biya musu bukatar su ko kuma su bar Najeriya, yayin da yankin Kudu maso Kudu ya shiga yanayi tababa da fargaba dangane da wannan yanayi.

Goyon bayan tattaunawa

Kungiyar ta bayyana goyan bayan tattaunawa ta kasa da kuma mika hannun ta ga yan siyasa daga bangarori da dama dake bukatar ganin an tsara irin kasar da ake bukata, ba tare da jiran zababbun yan siyasa domin tsara abinda ake bukata ba.

Sanarwar tace Yankin arewacin kasar ba zata bada kai bori ya hau ba wajen goyan bayan wasu yan siyasa saboda cimma muradun kan su ta kowacce hanya.

A karshe ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi amfani da karfin da kundin tsarin mulkin ya bashi na kare yankunan Najeriya da mutanen ta ko kuma ya amsa cewar ya gaza wajen jagorancin ta sakamakon dimbina matsalolin da suka addabe ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.