Isa ga babban shafi
Najeriya - Safarar Kwayoyi

NDLEA ta kame hodar Ibilis ta biliyoyin naira a Legas

Hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwaoyi ta NDLEA a Najeriya tayi nasarar kama wani fitaccen mai safarar kwayoyin Ejiofor Felix Enwereaku tare da kama hodar iblis na cocaine dauri 36 da nauyin ta ya kai kusan kilogram 28 da aka yiwa kudi naira biliyan 8 a tashar jiragen saman Murtala dake Lagos.

Hodar Ibilis
Hodar Ibilis © Zollfahndungsamt Hamburg/Handout via Reuters
Talla

Hukumar ta bayyana wanda ake zargin a matsayin wadanda suka yi suna wajen likawa jakankunan mutane kwayar ba tare da sanin su ba.

Kakakin hukumar Femi Babafemi yace sakamakon samun bayanan asiri jami’an hukumar sun yi nasarar damke wanda ake zargin bayan hodar da aka dauko daga Brazil ta biyo ta Addis Ababa dake Habasha zuwa birnin Lagos a jirgin Ethiopian airline.

Babafemi yace bayan sun kama kwayar a jakar da aka rasa mai ita, sai wanda ake zargin yaje neman jakar inda aka kama shi.

Jami’in yace wanda ake zargi ya amsa cewar ya bada Dala dubu 24,500 ga jami’an NDLEA domin ganin ya kubuta amma abin yaci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.