Al'amura sun tsaya cik a Oshodi dake Lagas bayan mamayar sojoji
Yanzu haka mazauna da fasinjoji na makale unguwar Oshodi dake birnin Legas, yayin da sojoji suka mamaye manyan wurare na unguwar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sunce jami’an sojan sun mamaye unguwar ce, da safiyar Alhamis don daukar fansar wani jami’in rundunar sojin saman Najeriya, wanda ake zargin wasu ’yan daba sun yi masa kisan gilla.
Al'amura sun tsaya
An lalata Motoci da dama, musamman na safa, yayin da wasu mutane suka fuskanci tsangwama daga fusatattun jami'an tsaro.
Wasu mazauna yankin da ke zuwa bakin aiki sun fada cikin rikicin yayin da dalibai suka tsere suka koma gida, kazalika 'Yan kasuwa sun tsare sun bar shagunsa, wasu kuma sun bar motocinsu kan titi.
Cunkuson ababen hawa
Lamarin ya kara tabarbarewar matsalar zirga-zirga a cikin wannan birni kasancewar yanzu babu wani motsi na shige da fitce daga bangaren na Oshodi inda sojojin suka mamaye.
Unguwar Oshodi ta haɗa wasu manyan sassan birnin Legas tana kuma dauke da babbar tashar motar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a shekarun baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu