Isa ga babban shafi
Najeriya - Tattalin Arziki

Babu surukuta tsakanin Buhari da wanda ake farauta kan batan dala miliyan 65

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce mutumin da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ICPC ke farauta kan satar dala miliyan 65 mai suna Gimba Kumo ba surikin shugaban kasar Muhammadu Buhari bane kamar yadda ake ta yayatawa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Bayanai sun ce Gimba Kumo da ya taba rike mukamin babban daraktan bankin kula da samar da gidaje na kasa, ya auri ‘ya ga shugaban Najeriya a shekarar 2016.

Sai dai kakakin shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya ce wannan alaka ta surukuta fa ta katse a shekarun baya.

Yanzu haka dai hukumar ICPC ne cigaba da neman Gimba Kumo da kuma wasu mutane biyu Tarry Rufus da ogunsola Bola ruwa a jallo, bisa tuhumarsu da yashe dala miliyan 65 daga baitulmalin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.