Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

Fadar shugaban Najeriya ta ce wasu na kitsa makircin kifar da gwamnatin Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta yi zargin cewar wasu tsoffin ‘Yan Siyasa da malaman addini na kitsa yunkurin kifar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ta hanyar amfani da karfi domin kawar da dimokuraradiyya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad
Talla

Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya raba wa manema labarai ta ce yanzu haka wadannan mutane na hayar magoya baya daga shugabannin kabilu da ‘Yan siyasa da zummar gudanar da wani taro da za su kada kuri’ar yankar kauna akan shugaba Muhammadu Buhari domin jefa kasar cikin rudani.

Adeshina ya bayyana yunkurin a matsayin haramtacce da kuma cin amanar kasa, inda yake cewa gwamnatin Buhari za ta kare Najeriya ta kowacce hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.