Isa ga babban shafi
Lagos-Abinci

Jihar Lagos na shirin rage dogaro da sassan Najeriya wajen samar da abinci

A wani sabon yunkuri na ganin ta rage dogaro da wasu sassan Najeriya da kuma kasashen waje wajen samar da abincin da jama’ar Jihar za ta ci, Gwamnatin Jihar Lagos ta kaddamar da wani gagarumin shiri da zai lakume tsabar  kudi sama da dala biliyan 10 a cikin shekaru 5 masu zuwa.

Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Gwamnan Jihar Babajide Sanwo Olu da ya kaddamar da shirin ya ce zai kunshi zuba jari a bangaren noma daga jama’a da 'yan kasuwa da masu zuba jari da kuma kungiyoyin ci gaba.

Sanwo Olu ya ce za su yi aiki tare da wadannan bangarori da zai taimakawa jama’a samun rance a kudin ruwa mara yawa tare da samun taimako, yayinda gwamnati za ta aiwatar da shirin da zai taimaka musu wajen bunkasa jarinsu.

Gwamnan ya ce shekaru 5 masu zuwa nan gaba za su zama wadanda za a yi aiki tukuru wajen rige rige ta hanyar bunkasa manufofin da aka shirya na ganin Jihar Lagos ta zama sahun gaba wajen samar da abinci a Najeriya.

Sanwo Olu ya ce yanzu haka suna aiki tare da wasu Jihohin da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya wajen samun filin noma, yayinda ya yi kira ga sauran jihohin da ke yankin kudu maso yamma da su ma su tashi wajen daukar irin wannan hanyar.

Gwamnan ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi ganin irin illar da annobar corona ta yi wa bangaren noma da samar da abinci.

Kafin wannan lokaci Gwamnatin Jihar Lagos da takwarar ta ta Jihar Kebbi sun kaddamar da noman shinkafa na hadin gwuiwa wanda aka kwashe shekaru da dama anayi wajen samarwa jama’ar jihohin shinkafa a farashi mai rahusa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.