Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

SERAP ta maka Buhari kotu saboda bacewar wasu kudaden bangaren lafiya

Kungiyar SERAP a Najeriya dake fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kai ƙarar shugaban kasar Muhammadu Buhari kotu kan abin da ta kira “kasa bincikar ɓacewar wasu kudade har sama da naira biliyan 3.836, da aka ware wa bangaren kiwon lafiya.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin wata ziyara da ya kai Katsina, ranar 18 ga watan Disambar 2020.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin wata ziyara da ya kai Katsina, ranar 18 ga watan Disambar 2020. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Cikin sanarwar da kungiyar ta fitar dauke da sahannun mataimakin shugabanta Kolawole Oluwadare ta ce ta shigar da ƙarar ne a babbar kotun Abuja inda take neman kotun ta tilastawa shugaban binciken kuɗaɗen da suka ɓata da kuma magance matsalar rashawa a ma’aikatar lafiya da asibitocin Tarayya da kuma Hukumar da ke sa ido kan abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC.

Shigar da karar na zuwa ne adai-dai lokacin da ake takaddama kan ziyarar da Shugaba Buhari ya yi zuwa Landan don duba lafiyarsa na yau da kullun, yayin da likitocin kasar ke yajin aiki a kan albashi da wasu hakkokinsu da ba a biya ba.

Yayin da abangare daya wasu ‘yan Najeriya mazauna Burtaniya suka gudanar da zanga-zangar adawa da ziyarar shugaban, tare da kira da ya koma gida don gyara asibitocin kasar, inda wasu suka yi ta tura masa ashar, lamarin da ya janyo tofin Ala tsine ga wadanda suka zagi shugaban ta kalmomi da basu dace ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.