Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane 2,619 a Zamafara cikin shekaru 8

Gwamnatin Zamfara a Najeriya ta ce mutane akalla dubu 2 da 619 ‘yan bindiga suka kashe sakamakon hare-haren da suka rika kaiwa sassan jihar.

Wani sansanin 'yan gudun hijirar da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa barin muhallansu a karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara.
Wani sansanin 'yan gudun hijirar da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa barin muhallansu a karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara. © MSF/Abayomi Akande
Talla

Yayin taron manema labarai jiya Juma’a a garin Kaduna, kwamishinan yada labaran jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya ce ‘yan bindigar sun salwantar da dubban rayukan ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2019.

Baya ga kuma mutane fiye da dubu biyun da suka kashe, Kwamishinan yace ‘yan bindigar sun sace wasu mutanen akalla dubu 1 da 190 da kuma dabbobi dubu 14 da 378 cikin shekaru 8.

Wasu 'yan Jihar Zamfara da hare-haren 'yan bindiga ya tilasta musu gudun hijira a wani gini dake karamar hukumar Anka.
Wasu 'yan Jihar Zamfara da hare-haren 'yan bindiga ya tilasta musu gudun hijira a wani gini dake karamar hukumar Anka. © Benedicte Kurzen/NOOR

Dosara ya kara da cewar kawo yanzu mutane sama da dubu 100 ne suka tsere daga muhallansu, sakmakon tashin hankalin ‘yan bindiga a sassan Zamfara, yayin da ita kuma gwamnatin Zamfara ta kashe naira miliyan 970 wajen biyan kudin fansar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Wani batu kuma da ya dauki hankula shi ne kokawar da gwamnatin Zamfarar ta yi kan adadin ‘yan bindigar dake addabar sassan arewacin Najeriya da ta ce ya kai dubu 30 a sansanoni fiye da 100 a jihar.

Sai dai  gwamnatin ta ce shirinta na sulhu da ‘yan bindigar zai ci gaba da gudana, la’akari  da muhimmancinsa  wajen maido tsaro a jihar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.