Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari zai koma Ingila don duba lafiyarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa Ingila domin duba lafiyarsa a gobe Talata kamar yadda fadarsa ta sanar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da hafsoshin tsaron Najeriya kafin tafiya Ingila a Talatar nan.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da hafsoshin tsaron Najeriya kafin tafiya Ingila a Talatar nan. AFP/Archivos
Talla

Mai magana da yawun fadar Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa, shugaban zai tafi birnin London na Ingila a ranar 30 ga watan Maris domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Kafin tafiyar tasa, Buhari zai gana da hafsoshin  tsaron Najeriya a sanyin safiyar Talatar, sannan ya dauki hanyar zuwa filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Abuja kamar yadda Adesina ya bayyana.

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da shirye-shiryen Buhari na komawa Ingila don duba lafiyarsa

Ana sa ran  Buhari zai koma Najeriya a cikin mako na biyu na watan Afrilun wannan shekara  kamar yadda sanarwar fadarsa ta ce.

A shekarar 2017 ne, shugaban ya shafe tsawon kwanaki 100 a birnin London, inda ya yi wata doguwar jinyar cutar da har yanzu ba a bayyana ta ba, lamarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen Najeriya.

Wasu daga cikin ‘yan kasar musamman daga bangaren ‘yan adawa sun bukaci shugaban da ya sauka daga karagar mulki a wancan lokaci da ya dade yana jinya a London.

Shugaban ya  dade bai yi tafiya zuwa kasar waje ba saboda annobar coronavirus wadda ta tilasta rufe kan iyakokin kasashen duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.