Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da Janar Abdulsalami kan halin da Najeriya ke ciki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yau ya gana da tsohon shugaban kasa Janar Abdusalami Abubakar dake fadar sa dake Abuja kan halin da Najeriya ke ciki ayau.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Bashir Ahmed ya sanar da ganawar shugabannin biyu ba tare da bayani kan abin da suka tattauna ba.

A kwanakin da suka gabata, tsohon shugaban kasar ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ta addabi sassan Najeriya, inda ya bayyana rashin amincewar sa da shirin tattaunawa da 'yan bindiga da ke sace mutane domin karbar diyya.

Janar Abubakar ya bukaci jami’an tsaron kasar da su kara kaimi wajen shawo kan wadannan matsaloli da ke yiwa Najeriya barazana.

Tsohon shugaban ya bayyana takaicin sa kan halin da kasar ta samu kan ta musamman yadda jama’a suka zama 'yan gudun hijira sakamakon hare haren 'yan bindigar.

Janar Abubakar ya bukaci gwamnonin jihohi da su kawo karshen korafin da su ke wajen daukar matakan da suka dace domin samar da zaman lafiya a jihohin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.