Isa ga babban shafi

Tinubu ya bukaci Buhari ya kira taron gaggawa kan rikicin fulani da Makiyaya

Tsohon Gwamnan Jihar Lagos dake Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kiran taron masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalar da ake samu dangane da rikicin Fulani makiyaya da manoma a sassan kasar.

Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu tare da Zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari
Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu tare da Zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Wannan ya biyo bayan rasa dimbin rayuka da dukiyoyin Yan Najeriya da ake cigaba da samu sakamakon wannan rikici dake neman rikidewa zuwa rikicin kabilanci.

Sanarwar da tsohon gwamnan kuma jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ya gabatar yau asabar ta bada shawarar gayyatar Gwamnonin jihohi da Sarakunan gargajiya da Jami’an tsaro da Shugabannin addinai da kuma wakilan manoma da makiyaya domin tattauna matsalar.

Tinubu yace ganin yadda aka samun matsalar da kuma tashin hankalin dake biyo baya, ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su gaggauta samo maslaha domin kawo karshen kashe kashen da ake samu da kuma asarar dukiyoyi.

Tsohon Gwamnan yace radadin matsalar tattalin arziki da yaduwar makamai a hannun jama’a da karuwar aikata laifuffuka da kuma gazawar hukumomin wajen shawo kan su sun taimaka wajen fadada yanayin da Najeriya ta samu kan ta ayau.

Tinubu ya bayyana cewar halin da makiyaya suke ciki ba abu ne da za’a amince da shi ba, yayin da harkokin su na kiwo ya sabawa halin da ake ciki a wannan zamani.

Saboda da haka tsohon Gwamnan yace wannan taro zai taimaka wajen bada shawara kan yadda za’a warware matsalar, yayin da Gwamnonin Jihohi suma zasu gudanar da nasu tarukan domin daukar matakan da zasu dace da yanayin su.

Domin samun nasarar wannan, Tinubu ya bukaci tabbatar da tsaro da kuma doka musamman a yankunan da ake fama da wadannan rikice rikice, da taimakawa makiyaya samo hanyar yadda zasu inganta harkokin su ta hanyar samun riba da kuma killace filayen da za’a bayar domin kiwo a farashi mai sauki.

Tsohon Gwamnan ya kuma bukaci taimakawa manoma wajen bunkasa harkokin noman su yadda zasu samu riba wajen basu tallafin taki da injinan kayan noma da kuma kafa hukumomin daidaita farashi kan amfanin gona masu muhimmanci.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.