Asirin 'yan gudun hijarar bogi ya tonu a Maiduguri
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya gano ‘yan gudan hijira na buge 650 a lokacin da ya kai ziyarar bazata wani sansanin 'yan gudun hijirar da ke birnin Maiduguri.
Wallafawa ranar:
Ziyar gwamna Zulum sansanin dake Kwalejin gwamnati na nazarin Shari’ar Musulunci na Mohammed Goni da ke Maiduguri babban birnin jihar, na zuwa ne bayan korafe-korafe na cewa dubban mazauna garin na ikirarin zama ‘yan gudun hijara a sansanin.
Sanarwar da mai taimakawa gwamna Zulum kan kafofin sada zumuntar yanar gizo Abdurrahman Ahmed Bundi ya wallafa a shafukansa, ta bayyana cewa 'yan gudun hijirar na bogi na wuni a sansanin lokacin da ake raba abinci, kuma su arce gidajesu cikin dare.
Ziyarar Bazata
Wannan ne yasa gwamna Babagana Zulum ya kai ziyarar bazata tsakar dare a ranar Lahadi, zuwa Kwalejin Mohammed Goni, inda ake kula da ‘yan gudun hijirar da suka tsarewa rikicin Boko Haram daga karamar hukumar Abadam da ke arewacin Borno suka yada zango.
“Aikin wanda ya ƙare da misalin ƙarfe 1 na dare, ya gano cewa a cikin magidanta 1,000 da jami’an agaji sukayi rajistansu amatsayin ‘yan gudun hijira 650 duk na bogi ne.’’
Gwamna Babagana Zulum wanda ya samu rakiyar shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, Air Commodore M.T. Abdullahi Kasa, da kwamishinoni biyu (Noma, da Kananan Hukumomi da Masarautu) ya gano ainin ‘yan gudun hijira 450 cikin 1000.
To fish-out fake IDPs, @ProfZulum storms camp midnight for headcount
— Governor Borno (@GovBorno) March 7, 2021
... Discovers 650 ghost households https://t.co/jAkZAwWdjq pic.twitter.com/hyRFY0cVAP
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu