Buhari ya karbi allurar rigakafin cutar Korona a birnin Abuja
Yau Asabar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo suka karbi allurar rigakafin cutar Korona a birnin Abuja.
Wallafawa ranar:
A jiya Juma’a gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da shirin yiwa ‘yan kasar allurar rigakafin ta Korona, inda aka fara daga kan ma’aikatan lafiya.
Ngong Cyprian wani likita a Najeriyar ne ya kafa tarihin zama mutum na farko da aka fara yiwa allurar da kamfanin AstraZeneca ya samar.
A halin da ake ciki, mutane dubu 1 da 954 annobar Korona ta kashe a Najeriya daga cikin akalla dubu 158 da suka kamu, yayin da kuma dubu 137 suka warke.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu