Isa ga babban shafi
Najeriya-MDD

IFAD ta taimakawa manoman Najeriya dubu 8 da tallafin kudi

Asusun Bunkasa noma na Majalisar Dinkin Duniya, IFAD da Gwamnatin Najeriya na wani aikin hadin gwuiwa da zummar ganin sun taimakawa kananan manoma da masu aikin samar da abinci a Yankin Arewacin Najeriya domin farfadowa daga illar cutar korona.

Wasu manoman shinkafa a Najeriya
Wasu manoman shinkafa a Najeriya IFAD
Talla

IFAD ta bada kashi na farko na tallafin Dala 900,000 ta hannun shirin ta na taimakawa mazauna karkara domin rarrabawa irin wadannan manoma domin sake farfadowa daga matsalolin da suka samu kan su a ciki.

Yarjejeniyar bada wannan taimako ya samu sanya hannu ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed da Daraktan IFAD dake kula da Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya Nadine Gbossa domin ganin mazauna Jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Katsina da Kebbi da Sokoto da Yobe da kuma Zamfara sun amfana.

A karkashin jagorancin ma’aikatar kula da ayyukan noma ta Najeriya kananan manoma sama da 8,000 ake saran suci gajiyar wannan shirin wanda zai rage radadin matsalolin da suke fuskanta sakamakon sauyin yanayi da annobar korona.

Ministan kula da ayyukan noma Alh Mohammed Sabo Nanono ya bayyana farin cikin gwamnatin Najeriya dangane da wannan taimako da IFAD ya gabatar wanda yace zai taimaka gaya wajen rage radadin da wadannan manoma ke fuskanta.

Nanono yace gwamnati zata sayi tan 80 na irin masara da shinkafa da kayan marmari da tan 722 na takin zamani domin rabawa kananan manoman.

Ministan ya bayyana cewar kashi 50 na manoman da zasu amfana da wannan tallafi mata ne, kashi 25 maza sai kuma matasa da zasu kai kashi 25.

Daraktan Hukumar IFAD Nadine Gbossa yace a shirye suke wajen ganin mata da matasa sun amfana da shirin da ya kaddamar na basu tallafi.

Daga shekarar 1985 zuwa yanzu, IFAD ta dauki nauyin ayyuka daban daban har kasha 11 a Najeriya da kudin su ya kai kusan Dala miliyan 115, cikin su harda Dala miliyan 510 na tsabar kudin da aka rabawa mazauna karkara miliyan 3 da dubu 900 a Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.