Isa ga babban shafi
Najeriya

Abin da na gani a ziyarar da na kai wa 'yan bindiga-Gumi

Fitaccen Malamin Islama na Najeriya, Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bada labarin abin da ya gamu da shi a yayin ziyarar da ya kai sansanonin ‘yan bindigar da ke jihar Zamfara.

Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi a yayin ziyartar 'yan bindiga.
Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi a yayin ziyartar 'yan bindiga. Daily Trust
Talla

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Gumi wanda ya damu da karuwar matsalar tsaro a yankin arewa maso yammaci, ya ziyarci tungar maharan tare da rokon su da su rungumi zaman lafiya.

A lokacin da yake yi wa gwamnan Zamfara Bello Mutawalle bayani a gidan gwamnati da ke birnin Gusau a ranar Alhamis, shahararren malamin ya ce, ‘yan bindigar sun zama ‘yan ta’adda ne sakamakon yadda jama’ar jihar ke daukar su.

Malamin ya roki gwamnatoci a dukkanin matakai da zu cimma zaman lafiya da ‘yan bindigar, yana mai cewa, tattaunawa ita ce zabi da ya tilo don kawo karshen matsalar.

“ A mafi akasarin sansanonin ‘yan bindigar da Fulani da na ziyarta a Zamfara, na fahimci cewa, ba komai ke faruwa ba a jihar illa ta’addanci.” In ji Gumi.

Malamin ya kara da cewa, "Wasu mutane na da ra’ayin yakar tare da kashe ‘yan bindigar, amma abin da muka fahimta shi ne cewa, akasarin su jahilai ne da ke bukatar ilmantarwa da wayar da kai."

Sheikh Gumi ya ce, "Mayawaita ‘yan bindigar da ya hadu da su sun zama miyagu ne saboda hare-hare da razanar da suke fuskanta daga kungiyar mayakan sa-kai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.