Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: 'Yan sanda 3, dogarai 5 sun mutu a harin da aka kai wa sarkin Kauran Namoda

‘Yan sanda a jihar Katsinar Najeriya sun ce jami’ansu 3 ne tare da dogaran sarki 5 suka mutu bayan wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa sarkin Kauran Namoda a jihar Zamfara, a ranar Juma’a.

Tamabarin 'yan sandan Najeriya
Tamabarin 'yan sandan Najeriya AFP
Talla

Tun da farko rahotanni daga Najeriyar sun ce mutane 8 sun mutu bayan da wasu ‘yan bindida suka afka wa ayarin sarkin Kauraan Namoda, Sanusi Muhammad.

Wani kawu ga sarkin, Abdulkarim Ahmad-Asha, ya tabbatar wa da jaridar PREMIUM TIMES aukuwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun bindige direban mota kirar Hilux da ke gaba, suka kuma kashe ‘yan sanda 3, da sauran mutane, wadanda dogaran sarkin ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isa, a wata sanarwa, ya tabbatar da asarar jami’ai 3 da suka yi sakamakon harin, inda ya ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana agogon Najeriya a kan hanyar Funtua zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.