Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Filato ya kamu da cutar coronavirus

Gwamnan Jihar Filato dake Najeriya Simon Lalong ya zama na baya bayan nan cikin fitattun mutanen da suka herbu da cutar korona sakamakon gwanin da aka masa.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong
Gwamnan jihar Filato Simon Lalong Twitter@sblalong
Talla

Mai magana da yawun gwamnatin Jihar Makut Simon Macham yace gwajin da aka yiwa Gwamnan da iyalan sa, ya nuna cewar shi yana dauke da cutar, amma kuma babu wani daga cikin iyalan są da ya harbu.

Sanarwar tace gwamnan ya killace kansa, kuma wannan zai bashi damar cigaba da aiki daga gida.

Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar yaki da cututtuka ta sanar da cewar Najeriya ta samu adadin da ba’a saba gani ba na masu dauke da cutar larabar nan, wadanda suka kai 930, kuma Jihar Plateau ce Jiha ta 3 mafi hawan jama’ar da suka kamu da ita.

Shima Gwamnan Jihar Lagos ya killace kan sa yanzu haka, yayin da gwamnatin Najeriya ke barazanar takaita zirga zirga saboda ganin yadda jama’a basa mutunta ka’idodin da aka gindaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.