Isa ga babban shafi
Najeriya

Masana na bukatar korar cocin Super Eagles ta Najeriya

Masana harkar tamola a Najeriya na ci gaba da nuna bukatar ganin anyi waje da mai horas da ‘yan wasan tawagar kwallon kafar kasar Super Eagles Genot Rohr.

Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Genot Rohr.
Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Genot Rohr. REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Na baya-bayan nan da yayi tsokaci shine, Tsohon dan wasan kasar Jonathan Akpoborie, wanda ya ce kocin na Super Eagles dan kasar Jamus bai cancanci sabanta kwantiragi sa ba sakamakon rawar da kungiyar ke takawa karkashinsa yanzu haka, masamman abin da ya faru a wasan da suka buga a jihar Edo, a neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.

A watan Mayu ne Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta bai wa Rohr sabon kwantaragin shekaru biyu wanda zai kai Bajamushen har zuwa shekarar 2022, a matsayin koci mafi tsawo a tarihin kasar.

Akpoborie ya yi amannar cewa Rohr ya zama tamakar wani nauyi ga kungiyar ta super Eagles, bayan kunnen doki da suka yi da Saliyo da ci 4 da 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.