Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Lagos za ta hana Tinubu kudinsa na fansho

Gwamnatin Lagos da ke Najeriya ta bayyana aniyarta ta sake fasalin dokar fansho wadda za ta soke kudin fanshon da ake bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakansu da suka yi wa jihar hidima, cikinsu har da jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Ayyuka, Babatunde Raji Fashola.

Bola Tinubu
Bola Tinubu REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya bayyana haka a zauren Majalisar Dokoki lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2021.

Sanwo-Olu ya ce nan gaba kadan zai gabatar da kudirin dokar ga majalisar domin amincewa da ita da zummar rage nauyin da ke wuyan gwamnati na biyan makudan kudade ga ‘yan siyasa a matsayin fansho.

Biyan fansho ga gwamnoni da mataimakansu na daya daga cikin hanyoyin da jihohi ke asarar tarin kudaden da suka dace a yi wa talakawa aiki da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.