Isa ga babban shafi

Afenifere da Soyinka sun yi watsi da barazanar korar 'Yan kabilar Igbo

Kungiyar Kare muradun 'Yan Kabilar Yarbawa ta Afenifere tare da Fitaccen marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka sun bukaci Yan Kabilar Igbo da suyi watsi da wa’adin sa’oi 48 da wata kungiyar matasan Yarbawa ta ba su na ficewa daga cikin birnin Lagos da yankunan Yarbawa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari  sanya da kayan kabilar Igbo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sanya da kayan kabilar Igbo RFIHAUSA
Talla

Shugaban kungiyar Afenifere Pa Reuben Fasonranti yace babu hannun kungiyar su cikin sanarwar korar Yan kabilar Igbon, yayin da suka yi watsi da kokarin sanya batun kabilanci cikin tarzomar da aka samu a birnin Lagos.

Fasoranti ya bukaci Yan kabilar Igbon da su cigaba da gudanar da harkokin su a Lagos da wasu biranen dake kudu maso yamma cikin kwanciyar hankali.

Shima Farfesa Wole Soyinka yayi watsi da sakon bidiyon da kungiyar matasan Yarbawan suka bayar na umurtar Yan kabilar Igbo su fice daga Yankin, inda ya bayyana wanda ya gabatar da sakon a matsayin mahaukaci.

Soyinka ya bayyana sakon a matsayin abin kunya da ya fito daga wajen mara hankali wanda ke neman raba kan al’ummar kasa.

Shugaban kungiyar matasan Yarbawa dake neman Yanci da ya kira kan sa ‘Adeyinka Grandson’ dake kuma zama a Turai, yace muddin Yan kabilar Igbo suka ki ficewa daga Lagos tsakanin juma’a zuwa yau lahadi, daga gobe zasu rufe daukacin hanyoyin mota da hana motoci shiga yankin domin daukar mataki kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.